MAGANIN gargajiya na hawan jini, ciwon suga da sauransu

 Isyaku Garba Zuru 06-01-2020
Ko ka san cewa masana ilimin kimiyyar magunguna na Kasar Sin da India sun tabbatar da cewar daya daga cikin manyan magungunan  warkar da ciwon suga (diabetes) shine ganyen mangwaro?
Ganyen magwaro na dauke da sinadarai masu yawan gaske da ke amfana wa jikin Dan’adam, amma kash! Mutane da dama basu sani ba.

Yadda ake amfani da shi a matsayin maganin cutar suga ( Diabetes)

(1) ka tsinko ganyan mangwaronka masu kyau  sai ka wanke su sosai
(2) Ka sanya ruwa a murhu ka tafasashi har na tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba.
(3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin  da ke kan murhu  tare da  OLIVE oil  wato man Zaitun, a barshi yayi ta tafasa har na tsawon mintuna biyar zuwa goma.
(4) Sai a sauke shi a tace
(5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau a barshi ya kwana
(6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan ka tashi daga barci, kafin ka ci komai.

Wannan maganin, yana kawar da abubuwa marasa kyau masu guba daga jikin mutum, kuma yana rage yawan suga da ke cikin jini. Yana kuma  saukar da hawanjini sosai.

Haka kuma yana  taimakawa matuka wajen  kwantar da tari, ASTHMA, yakan sa ka samu numfashi mai kyau mai sauki. 

Zaman dar-dar ko rashin nutsuwa sosai (restlessness), Idan ka zuba cokali biyu ko uku a cikin ruwan wankan ka, sannan kayi wanka dashi, yana sanya kaji jikinka garau kuma kaji hankalin ka ya kwanta soasai.

Dutsen dake cikin hanta ko Madata ko Koda (wato kidney stone), mai wannan ciwon zai iya busar da ganyen mangwaro a inuwa sannan a daka shi a zuba garin acikin kofi/glass ko kwano a barshi ya kwana a rinka sha kullum da safe. Wannan yana narkar da dutsen dake jikin koda sosai.


Tari da Gushewar Murya ko Asthma ,

A dafa ganyen Mangwaro a sanya masa Zuma kadan yana taimakawa kwarai da gaske cikin sauri.
Attini ko kashi da jinni,
Sai a  shanya ganyen a inuwa a busar dashi a mayar dashi gari, a rinka sha sau uku a rana . Yana tsayar da  wannan cutar.

Ciwon Kunne

Idan aka tatse ruwan ganyen mangwaro aka dan dafa shi, sai a rinka digawa a cikin kunnen. Wannan na maganin ciwon kunne.

Kunar Wuta

Sai a kona ganyen mangwaro har ya zama toka, sai a rinka barbadawa a wurin da aka kone, yana warkar da kunar cikin sauri zai bushe In Sha-Allahu.
Shakuwa da ciwon makogoro
Idan kana shakuwa ko zafin makogwaro. Sai ka kona ganyen mangwaro ka shaki hayakin, yana maganin tsayar da shakuwan da kuma ciwon makogwaro.

Ciwon ciki

Idan kana yawan ciwon ciki sai ka sanya ganyen mangwaro a cikin ruwan dimi ka barshi ya kwana sannan ka sha da safe kafin kaci komai. In ka juri yin hakan zai warkar maka da ciwon ciki kowane iri ne  in Allah Ya yarda. 

Shan ganyen mangwaro a kai a kai yana kuma  kara inganta garkuwan jiki kuma yana maganin hana kumburin ciki. Yana da kyau ka jurewa shan wannan ganyen mangwaro a duk safiya domin ganin yadda  suga dake cikin jikin ka zai sauka cikin sauri. Allah (SWT) yasa mudace. 
(Tuntubi likitanka kafin ka soma shan kowane irin magani).

Zan cigaba da kawo muku amfanin ganyayen da muke dasu a gidajenmu ko kewayenmu wajen warkar da cututtuka daban-daban in Allah ya yarda kamar yadda masanan magungunan gargajiya na Kasar Sin suka gano.

Daga Balarabe Shehu Illelah, Kasar Sin (China)

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari <
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN