Yadda aka kashe mutum 2 aka kone gawakinsu a kasuwar Dadin kowa jihar Kebbi

Fusatattun jama'a da suka je cin kasuwa a garin Dadin kowa da ke karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi ranar Lahadi 26 ga watan Janairu 2020, sun kashe wasu mutum biyu, suka kone gawarsu, bisa zargin kasancewa yan fashi da sace mutane, watau Kidnapas (Kidnappers).

Rahotanni sun ce, wani Bafulatani ne ya gane daya daga cikin wadanda yake zargin sun yi masa fashi yayin da mutumin yake sayayya a cikin kasuwar, daga bisani Bafulatani ya yi kuwar "Barawo", lamari da ya ja hankalin mutane suka zo wajen.

Majiyarmu ta ce, bayan jama'a sun fara dukan wanda Bafulace ya zarge shi da yi masa fashi bayan sun yi masa gajeruwar tambayoyi, sai wanda ake duka ya ce ai ba shi kadai bane, ya gaya wa jama'a inda za a sami na biyun a cikin Kasuwar, kuma shi ma aka kamo shi aka hada da na farkon aka yi masu duka har rai ya yi halinsa a bainar jama'a. Daga bisani aka banka wa gawakinsu wuta har suka kone kurmus.

Hakazalika majiyarmu ta ce, lokacin da jami'an yansanda suka je wajen, har an kashe mutanen kuma an kone su. Amma daga bisani yansanda sun kwashe gawakin mutanen, suka kai su Asibitin Maiyama, inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Matsalar Kidnapas dai na kara zama barazana a jihar Kebbi, musamman a Masarautar Gwandu da ta fi yawan kananan hukumomi a cikin Masarautu hudu da ke fadin jihar
 

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN