Wani matashi ya yi mutuwar gaggawa yana tsakiyar aikata zina da budurwa a daki

Wani matashi ya mutu a cikin dakin wani Otel lokacin da yake lalata da wata budurwa a birnin Onitsha na jihar Anamra.

Rahotanni sun ce matashin ya shiga dakin Otel da wata budurwa ranar Alhamis da misalin karfe 5 na yamma.

Amma ba a wuce minti 30 ba sai aka ji ya fara ihu, yana cewa a zo a taimakeshi yayin da ya rike kirjinshi dam a cikin yanayin ciwo.

Nan take Manajan wannan Otel ya saka shi a mota aka garzaya zuwa Asibiti da shi, daga bisani Likitoci suka ce ya mutu.

Yansandan sashen CPS sun je wajen da lamarin ya faru, kuma sun dauki hotuna, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kakakin rundunar yansandan jihar SP Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Babu bayani ko an gane budurwar da matashin ya shiga dakin Otel tare da ita, haka zalika babu labari ko an kamata.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari