Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

Rahotun Jaridar Legit Hausa

Wata mata mai matsakaicin shekaru ta shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Katsina a karamar hukumar Malumfashi bayan zarginta da aka yi da sokawa mijinta wuka. A take kuwa ya sheka lahira. Lamarin ya faru ne a kauyen Danjaku da ke karamar hukumar Malumfashi kamar yadda jaridar Katsina Post ta ruwaito.

Marigayin wanda aka bayyana sunansa da Malam Shamsu ya mutu ne bayan da aka garzaya da shi asibitin Galadima Abdullahi da ke Malumfashi. Matar wacce har yanzu ba a gano sunanta ba an gano cewa ta halaka Malam Shamsu har lahira ne bayan da wata 'yar hatsaniya ta sarke tsakaninsu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa an kama wacce ake zargin. Wannan na faru ne jim kadan bayan da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta halaka mijinta Bilyaminu Halliru har lahira.

Kotun ta kama Maryam da laifin kashe mijinta kuma an tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake mata. Za'a ajiyeta a gidan kurkukun Suleja har ta gama daukaka kara. Bayan Yusuf Halilu, ya kama Maryam Sanda, da laifin kashe mijinta, an yi wani gajeran rikici a cikin kotun.

Alkali Yusuf Halilu na furta cewa an kama ta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda ta arce daga cikin akwatin mai laifi a kotu amma ma'aikatan gidan Kurkuku da kotun suka damkota.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN