Akalla mutum uku sun mutu, kuma aka kone gidaje da dama sakamakon wani tashin hankali da ya auku tsakanin kabilar Tiv da na Fulani a kauyen Pangari da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba kamar yadda jama'ar gari suka shaida wa jaridar Punch ranar Litinin.
Wani ganau ba jiyau ba mai suna Pius Gura, ya gawa wa manema labarai cewa lamarin ya samo asali ne bayan an yi zargin cewa wani Makiyayi ya shiga gonar wake mallakin wani Manomi mai suna Mr, Dooior James dan kabilar Tiv, kuma dabbobinsa suka mi masa barna, bayan sun ci wake mai yawa sai Manomin ya nemi Makiyayin ya biya shi barna da dabbobinsa suka yi masa a gona.
Daga bisani Makiyayin ya zare adda ya sare Manomin kuma ya mutu nan take. Jin labarin ke da wuya sai yanuwan Manomin suka hadu suka bi Makiyayin, shi ma suka kashe shi. Wannan ne dalili da ya sa lamarin ya kazamce. Domin bayan yanuwan Makiyayin sun sami labarin abin da ya faru da danuwansu, sai suka yi gangami suka je suka kone gidaje da dama tare da kashe mutum uku a rikicin.
Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Bali, Yarima Musa Mahmood, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce mutum uku ne suka mutu a rikicin. Ya kuma ce an sami zaman lafiya a garin bayan isowar jami'an tsaro.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari