Jarumar masana'antar finafinai na Nollywood Princess Shyngle ta yi wani babban fallasa yadda sauran Jarumai mata a masana'antar ke samun makuddan kudade a rayuwarsu wanda ta ce sun dade suna boyewa.
Ta ce Jarumai mata basu samun kudi kawai domin sun fito a wasannanin fina finai.
Jaruma Princess ta yi zargin cewa Jarumai mata kan bayar da kansu ne ga attajiran mutane wadanda ke mutukar begensu.
" A ko da yaushe na wallafa hotuna da ke bayyana surar jikina, Email nawa yakan cika da masu neman yin lalata, kuma a shirye suke su biya, ko su kashe kudi ko nawa ne domin su saami biyan bukata'.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari