Bayan tarnaki da kangi da takunkumi da aka dora wa kasar Iran ya yi tasiri a kan shirinta na kera rokokin yaki da makamai masu linzami, amma yanzu shirin ya sami gagarumar nassarar bunkasa a masana'antar kere-keren makaman yaki da sojin kasar ke kerawa da kansu.
Masana kan tsare tsaren kariyar tsaron kasa da kasa sun yi hasashen cewa kere keren makamai masu linzami masu cin karami da dogon zango na kasar Iran sun fi guda 200 wanda ke karkashin kulawan zaratan sojin juyin juya hali na Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC} na kasar Iran.
A yiwuwar isa nisan zangon kilomita 2,500km watau (Mil 1.500 miles) sabon makami mai linzami na kasar Iran wanda aka inganta shi da sinadarin mai na kimiyya wadatacce, baya bukatar dogon lokaci wajen harbawa, kuma zai ci dogon zango da zai iya fadawa a kan wajen da ake bukatan kai hari a gabas ta tsakiya cikin sauki.
Wani abin da ya ba masana da masu kula da harkar tsaron kasa da kasa shine irin yadda kasar Iran ta kware tare da bunkasa kan yadda ta kera makaminta mai linzami sumfurin Hoyeyzed wanda ke cin tafiyar nisan kilomita 1.300km (Mil 808) sama kadan daga doron kasa ba tare da an gane ba har ya isa wajen da ake bukatar kai hari.
Za a iya ganin tasirin wannan makami mai linzami a wani hari da yan tawayen Houthi na kasar Yamen wanda ke samun taimakon makamai daga Iran suka yi ikirarin kaiwa a kamfunan hakan mai na kasar Saudiya kai tsaye cikin nassara, a mataki daya tilau na hari da makamin ya sauka kuma daidai inda ake bukata.
Wannan nassara ya nuna yadda makamai masu linzami kirar kasar Iran suka wadatu da tsarin zamani, a mataki na iya amfani da su a kowane irin yaki da Iran za ta sami kanta a wanna zamani.
Rahotun Isyaku Garba Zuru
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari