Wani hadimin Gwamnan jihar Kebbi ya maka Mawakan jihar Kebbi a Kotu

Wani hadimin Gwamnan jihar Kebbi Dr. Haliru Bala, ya yi karar Mawakan jihar Kebbi a gaban wata Kotun Majistare da ke garin Birnin kebbi bisa zargin Mawakan da cin zarafinsa da Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, iyalinsa, hadimai da aminansa, tare da Gwamnatin jihar Kebbi.

ISYAKU.COM ya samo cewa hadimin Gwamnan, ya yi karar ne ranar 7 ga watan Janairu kwana daya kafin wasu Mawakan su gurfana a gaban Kotun Majistare, sakamakon kara da Gwamnan jihar Kebbi ya shigar a gaban Kotu, wanda ke dauke da koken kara kwatankwacin irin wanda Dr Haliru ya shigar a kan Mawakan.

Tuni Mawakan suka yi hayan Lauyoyi domin kare su a gaban Kotu bisa tuhuma da suke fuskanta kan zargin cin zarafi da mutuncin Gwamnan Kebbi da hadimansa a cikin wakar da suka rera.

Sai dai kawo yanzu, Kotu bata sa ranar sauraron kara da Dr. Haliru ya shigar ba a gabanta kawo yanzu da muka wallafa wannan rahotu.

Sai dai za a ci gaba da shari'ar da Gwamnan jihar Kebbi ya shigar kan Mawakan ranar 9 ga watan Janairu a babban Kotu Majistare da ke garin Birnin kebbi.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN