Wani Mawakin jihar Kebbi ya sha zafafan mari 2 a hannun dan bangan siyasa

Wani Mawaki mai suna Dan Galadima (Dan deko) a garin Birnin kebbi na jihar Kebbi, ya sha mari biyu masu zafi a wajen wani dan bangan siyasa a unguwar Rafin Atiku da yammacin ranar Asabar.

ISYAKU.COM ya samo cewa dan bangan siyasan ya sami Mawakin ne a Majalisi da yake zama da takala, zagi na fitan albarka da cin mutunci. Amma da yake Mawakin bai tanka masa ba sai ya zare hannunsa ya lafta wa Mawakin mari har sau biyu, daga bisani ya gudu.

Wani ganau ba jiyau ba wanda baya son a ambato sunansa, ya tabbatar mana da faruwar lamarin.

Kokari da muka yi domin samun dan bangan siyasan domin jin ta bakinsa amma mun kasa samun sa .

Wannan yana faruwa ne bayan nau'in tarzoma da ya kunnu kai inda wasu yan bangan siyasa suka yi amfani da matsayin uban gidansu suna daukan doka a hannunsu ta hanyar duka da cin zarafin wasu takakawan jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN