Wani magidanci ya mutu yayin da yake zina da wata mata a Otel

Rahotun Legit Hausa

Rundunar 'yan sandan jihar Delta a ranar Juma'a sun tabbatar da mutuwar wani mutum a wani otal dake yankin Ibusa. Kakakin 'yan sandan hukumar, DSP Onome Onovwakpoyeya ta sanar da manema labarai a garin Asaba cewa lamarin ya faru ne a Alhamis.

Tace hukumar otal din ne suka kai wa 'yan sandan yankin Ibusa din rahoto. Onovwakpoyeya tace: "mun samu rahoton aukuwar lamarin kuma jami'anmu sun je inda abun ya faru tare da dauke gawar.

A halin yanzu mun fara bincike a kan lamarin." Majiyoyi sun bayyana cewa ana zargin mutumin ya mutu ne bayan ya dau karuwa wacce ya kwanta da ita. Mamacin mai shekaru 55 har zuwa mutuwar shi direban mota ne. "Mutumin yana da aure kuma yana zaune da iyalanshi a Ibusa.

A ranar da abun ya faru, yaje otal din da wata mata mahaifiyar yara uku. "Matar ta fita daga dakin daga baya inda ta sanar da hukumar otal din da su duba mutumin don bashi da lafiya.

A nan ne kuwa aka gano mutumin baya motsi wanda hakan yasa aka kira hukuma," daya daga cikin majiyar ta sanar. Majiyar da ta nemi a sunanta ta bayyana cewa matar ta gudu bayan fita daga otal din amma 'yan sanda sun kama ta daga baya.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN