Kotu ta daga shari'ar Mawakan jihar Kebbi, ta ce yansanda su adana su zuwa washegari

Wata babban Kotun Majistare a garin Birnin kebbi, ta tasa keyar Mawaka uku daga cikin Mawaka 18 da Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya yi karansu a gabanta zuwa wajen yansanda kafin su sake bayyana a gabanta ranar 9 ga watan Janairu 2020.

Gwamna Bagudu ya yi karan Mawakan ne bisa zargin cin zarafinsa a wakoki da suka rera, wanda yake zargin sun ci zarafinsa tare da neman tursasa wa masoyansa su basu makuddan kudi, kamar yadda yake kunshe a takardar kara da aka gabatar a gaban Kotu.

Daga cikin Lauyoyi da suka tsaya wa Mawakan a gaban Kotu, sun hada da Barista A.A Fingilla, Nura Bello, Muhammad Nuruddeen, Ahmad I. Chiroma, da Mudassir Saleh. Yayin da Mawaka da suka gurfana a gaban Kotun sun hada da Musa Na' Allah (Mai shinkafa), Ibrahim S. Fulani da Muhammad Sani (MSani).

Tun farko Barista Muhammad Nuruddeen, ya kalubalanci yadda aka gabatar da kara a gaban Kotun tare da nuni bisa hurumin Kotu a wannan shari'a.

Haka zalika, Barista Nura Bello ya gaya wa Kotu cewa ba a ba wadanda aka yi kara sukunin samun wadataccen lokaci domin su shirya wa shari'a ba kamar yadda yake a tsarin dokokin shari'a na Najeriya.

Ya ce " Ya mai shari'a, an kama wadanda ake kara ne jiya, kuma aka gabatar da su a wannan Kotu a yau. Ba a basu dama ba ta yadda za su sami lokacin da za su shirya wa shari'ar kamar yadda yake a doka".


A nashi bayani ga Kotu, Barista A.A Fingilla ya ce " Rashin bayyanan mai kara a wannan shari'a ya nuna cewa bai dauki karar da ya yi da muhimmanci ba. Tunda yana da lokacin zuwa ko ya aiko a shigar da karan Mawakan da sunansa bisa tsarin shigar da karan kai tsaye na Direct Criminal Complain DCC,. Ya kamata kamar yadda ya sami lokaci ya yi kara sai ya sami lokaci ya zo Kotu ya kare karar da ya shigar a gaban Kotu.".

Fingilla ya kara da cewa " Wannan Kotu bata san waye Sanata Atiku Abubakar Bagudu ba a matsaayin Gwamna. Domin babu inda aka rubuta cewa (Mai girma Gwamna) a sunansa da yake rubuce a takardar koke a Kotu."

" A matsayinsa na Sanata kamar yadda yake rubuce a sunasa a cikin takardar koke a gaban Kotu, watau yana da sararin da zai dauki Lauya mai darajan SAN koda guda nawa yake so. Rashin zuwansa a Kotu, ko ya aiko wakili na Lauya, ko mai gabatar da kara na yansanda watau Prosecutor, ya nuna cewa yana shakka a kan abin da ya gabatar a gaban Kotu. Sakaamakon haka ina rokon Kotu ta daga shari'ar har illa masha Allahu duk ranar da ya shirya sai ya zo gaban Kotu domin a ci gaba da shari'ar.

Alkalin Kotun, babbaana Majistare Sama'ila K. Mungadi, ya daga shari'ar zuwa ranar Alhamis 9 ga watan Janairu domin ci gaba da saauraron shari'ar, yayin da ya yi umarnin cewa a kai Mawakan wajen yansanda har zuwa rana ta gaba sai a mayar da su a gaban Kotu domin ci gaba da shari'ar.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN