Wanda aka kama da layin wayar 'diyar shugaban kasa ya tona wa kansa asiri da kansa

Rahotun jaridar Legit Hausa

An samu bayanai game da wani Bawan Allah da ake zargin cewa an same shi ya na amfani da wani layin waya na ‘Diyar shugaban kasa, ya na aikata ta’adi. Bayanai sun fito game da labarin wannan mutumi da jami’an tsaro su ka cafke sa.

Kamar yadda mu ka samu labari, ainihin sunansa shi ne Mista Okolie Anthony. Okolie Anthony ya bayyana cewa kwadago ya ke yi na aikin gini ya na samun kudi. Kafin nan ya ce ya taba zama dilallin caca amma ya hakura da sana’ar daga baya.

Mista Anthony yanzu haka ya na kiwon kifi ne ya na samun kudi tare da wani Mutumi a gidansa da ke cikin Kauyen Oktuogwu a Garin Asaba da ke jihar Delta. Wannan mutumi ya ce ya samu wannan layin waya mai dauke da sunan Hannan Buhari ne a wajen mutumin da ya ke kiwo a gidansa, bayan shi ya sayi layin a titi.

Jami'an tsaro sun kama wanda ya ke amfani da tsohon layin wayar Hannan Buhari Source: Facebook Okolie ya nuna cewa ya yi mamaki bayan ya fahimci cewa lambar wayarsa ta 09035666662 ta na nuna sunan ‘Diyar shugaban kasa da zarar an bincika a waya. Jaridar Vanguard ta ce Okolie Anthony ya samu kan sa a matsala ne bayan da ya rika amfani da wannan lambar waya ya na yaudar mutane da sunan Hannan.

“A Ranar 21 ga Watan Yulin 2019, aka kama ni bayan na yi amfani da layin na aikawa wani sako ina neman taimakon kudi, kuma ya yi alkawarin zai ba ni.” “Ban sake yi masa magana ba, domin ban san wanene shi ba, ba.” Okoli ya shaida wannan da bakinsa. A karshe ya karyata cewa ya nemi ya kashe kansa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN