Allah ya yi wa Alhaji Sada Ilu rasuwa a birnin Cairo na kasar Egypt watau Misira . Jigo a jam'iyar APC a jihar Katsina kuma tsohon Darakta a hukumar tsaro na farin kaya DSS.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana marigayi Sada cewa rayuwarsa abin koyi ne ga al'umman jihar Katsina a wata sanarwa da ta fito daga hannun Darakatan watsa labarai na gidan Gwamnati Abdu Labaran ranar Lahadi.
Sada ya rike mukamai da dama a lokacin aikinsa a DSS, kuma daya daga cikin wadanda yan arewacin Najeriya a hukumar suka amfana matuka da shi sakamakon yadda ya ke yin tsaye ka'in da na'in domin ganin ba a zalunci yan arewa ba a hukumar.
Duniyar tsofaffin ma'aikatan hukumar DSS masu murabus za su tuna da karamci, mutunci, taimako da martaban Sada Ilu har iya rayuwarsu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari