Dalilin da yasa ba zan saki El-Zakzaky ba – El-Rufai

Rahotun Legit Hausa

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce ba zai saki Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria, (IMN), wacce aka fi sani da shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ba saboda radadin da shi da magoya bayansa suka sanya a zukatan mutanen jihar Kaduna tsawon shekaru 30 kafin a kama shi.

El-Rufai wanda ya yi magana a wata hira da gidan radiyo a ranar Juma’a, ya yi bayanin cewa makomar Shugaban kungiyar ta IMN baya a hannun gwamnatin jihar Kaduna cewa a hannun kotu ya ke.

Ya ce abunda gwamnatin tarayya ke nufi lokacin da ta ce makomar El-Zakzaky na a hannun gwamnatin jihar Kaduna shine cewa ba ita bace a kotu da Shugaban na IMN a yanzu. Gwamnan ya yi bayanin cewa bayan gwamnatin tarayya ta kama tare da tsare Shugaban na IMN a 2015, gwamnatin jihar Kauna da ta tuna zargin laifuffukan da Shugaban na IMN da magoya bayansa suka aikata a kan mutane da gwamnati tsawon shekaru 30, sai ta gudanar da wani bincike cikin rashin bin dokarsu, cin zarafin sauran mutane daga lokacin da suke birnin Zaria har zuwa lokacin da suka dawo Gellesu Quarters.

A koda yaushe mambobin IMN basa yarda da aikata laifi maimakon haka sai suka zargi gwamnati da kai masu hare-hare.Gwamnan ya ce duk kungiyoyin kasashen waje da suke sanya baki a lamarin suna bata wa kansu lokaci ne domin cewa wahalhalun da El-Zakzaky da mutanensa suka sanya mutanen Kaduna ciki yana da yawa on haka gwamnatin jihar ba za ta sake shi ba har sai kotu ta yanke hukunci.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN