Wakar batancin siyasa: An yi karar mawakan jihar Kebbi a gaban Kotu 3 sun shiga hannu

Mawakan siyasa na jihar Kebbi da suka rera wakar batanci ga wani babban dan siyasa a jihar Kebbi sun fara fuskantar fushin hukuma sakamakon kara da aka shigar a wata Kotun Majistare a kan cin zarafi da suka yi a wakokinsu.

Bisa umarnin Kotu, sakamakon shigar da kara da aka yi a gabanta, Kotu ta umarc yansanda su gudanar da bincike, lamari da ya sa jami'an tsaro sashen bincike CIID na yansanda suka gayyaci mawakan, an sami uku daga cikinsu kuma suna fuskantar bincike.

Mawakan na jihar Kebbi.da ke fuskantar bincike kawo yanzu sun hada da Musa Na' Allah (Mai shinkafa), Ibrahim S. Fulani da Muhammad Sani (MSani) yayin da har yanzu ba a sami sauran Mawakan ba.

ISYAKU.COM ya samo cewa an yi karaar Mawaka 18 ne a Kotun, amma kawo yanzu an sami 3 daga cikin adadin. Sai dai majiyarmu ta ce yansanda za su mika sakamakon bincike da Kotu ta umarcesu su yi da zarar sun kammala binciken.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN