Duba abin da aka gan tsohon shugaban kasa Obasanjo yana yi tare da lebarori a gonarsa

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo kenan tare da sauran manoma a kauyen Ibegun Olaogun kusa da Ifo a jihar Ogun yayin da yake girbe doya a gonarsa.

Wasu hotuna sun bayyana yadda Obasanjo tare da ma'aikata a gonarsa suka duka suna girbe doya.

Obasanjo wanda a zamanin mulkinsa na soja da farar hula, ya bayar da muhimmanci kan aikin gona, sakamakon haka ya fito da shirin Green Revolution da Operation Feed the Nation.

Hakazalika Obasanjo ya sha ba shugaba Buhari shawara cewa ya bayar da muhimmanci kan fannen aikin noma, watau Agriculture a Turance.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN