Cin zarafi: Gwamnan jihar Kebbi ya roki Kotu ta bi masa hakkinsa kan Mawakan jihar

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi karar Mawakan jihar Kebbi a gaban babban Kotun Majistare da ke garin Birnin kebbi yana rokon Kotu ta bi masa hakkinsa bisa cin zarafi da ya ce Mawakan sun yi masa a wakokin da suka rera.

A cikin koke da ya gabatar a gaban Kotu, Gwamna Babudu ya ce " Mawakan sun yi amfani da wakarsu domin su tilasta masoya na su basu makuddan kudi".

Ya kuma kara da cewa  "A ci gaba da yunkurinsu na bata mani suna matata, da Gwamnatin jihar Kebbi, Mawakan sun yi hira da harshen Hausa inda suka tabbatar da aniyarsu na yin haka" inji takardar koken.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN