Wakar batanci: Bidiyon yadda aka kai Mawakan jihar Kebbi Kurkuku

Babban Kotun Majistare karkashin Mai shari'a Samaila K. Mungadi, ranar Laraba 22 ga watan Janairu 2020, ta tasa keyar Mawaka guda 5 da Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu ya shigar a gabanta yana rokon Kotu ta bi masa hakkinsa bayan ya yi zargin cewa Mawakan sun ci zarafi, tare da bata sunansa, na iyalinsa da kuma Gwamnatin jihar Kebbi.

Bayan doguwar muhawara tsakanin Lauyoyin mai kara da na Mawakan, Mai shari'a Samaila Mungadi bai bayar da belin wadanda aka yi kara ba. Ya kuma bayar da umarnin cewa a kai su Kurkuku har zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu, yayin da Kotu zata duba takardar neman belin wadanda aka yi kara ranar 30 ga watan Janairy 2020.

Duba yadda aka tafi da Mawakan zuwa Kurkuku:



Mawaka da aka kai Kurkuku sun hada da Musa Na' Allah (Mai shinkafa), Ibrahim S. Fulani da Muhammad Sani (MSani), Malami Jabbi da kuma Nafi'u Gwadangaji.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN