Wani attajiri a Najeriya zai kawar da sauro har abada

Rahotun Legit Hausa

Ned Nwoko, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar jihar Delta ta Arewa a majalisar wakilai, ya ce ya shirya tsaf da matuka jirgin da zasu yi wa Najeriya feshi gabadaya. A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Nwoko ya ce feshi ne kadai zai kawo karshen sauro a kasar nan tare da tabbatar da fatattakar cutar Malaria ta har abada.


Kamar yadda wani rubutu da aka wallafa a shafinsa na kan shi ya bayyana, za a dau nauyin jami'o'i biyar a nahiyar Afirka da zasu yi bincike don habaka riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

 "Gidauniyar Ned Nwoko ta shirya tsaf don fatattakar cutar zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka kafin shekarar 2030," rubutun da aka wallafa ya ce. "Mataki na farko na cimma hakan shi ne feshi a Najeriya da sauran kasashen Afirka don kawo karshen sauro a Afirka.

Don cimma wannan manufa, za a yi taro da masu ruwa da tsaki kuma za a nada jakadai da jami'ai don hakan." in ji gidauniyar "Mataki na biyu kuwa shine kirkiro da hanyar kirkiro riga-kafin cutar zazzabin cizon sauron. Gidauniyar Ned Nwoko za ta dau nauyin binciken riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a manyan jami'o'i biyar na nahiyar Afirka." ta kara da cewa.

Nwoko wanda cikin kwanakin nan ya nufa Antarctica, ya ce ya zabi nan ne don ya jawo hankali a kan yakin korar zazzabin cizon sauro a Najeriya da Afirka. "Babban aiki ne da muka shirya tabbatar da shi. Zaku iya tunanin cewa Najeriya ta yi girman da ba za a iya yi mata feshi ba amma zamu yi kuma za ku gani," in ji shi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari