Waiyazu billahi: Uwargida ta banka wa kanta wuta ta mutu domin miji ya yi amarya

Wata matar aure mai suna Rabi, ta banka wa kanta wuta saboda mijinta ya auri Amarya a garin Gayawa da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano

Rahotanni sun ce, mijin Rabi mai suna Badamasi, ya yi sabuwar Amarya, lamari da uwargida bata so ba, kuma sakamakon kishi ta banka wa kanta wuta.

Yan uwa da abokan arziki, sun yi bakin ciki da nuna alhini, yadda Rabi ta kasa rike kanta har ta bari bakin kishi ya sa ta kashe kanta da kanta.


Kakakin yansanda na jihar Kano DSP Abdullahi Haruna, ya gaya wa manema labarai cewa yana kokarin ya tuntubi DPO na karamar hukumar kafin ya yi bayani, amma har zuwa lokacin rubuta wannan rahotu bai nayar da martani ba.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN