Daga karshe, ta bayyana cewa Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar , Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, Mawaki kuma jarumi a Masana'antar Kannywood, kuma daya daga cikin manyan Mawakan APC na Najeriya Yusuf Haruna, wanda ake ma inkiya da "Baban Chinedu", tare da tawagarsa, yayan Gwamnan jihar Kebbi Alh. Bello Bagudu, tare da sauran mutane ne suka taka rawa ta karshe da ya kai ga nasassarar sakin Mawakan jihar Kebbi da Kotu ta kai Kurkuku.
Duk da yake wata tawaga ta manyan Mawaka karkashin shahararren Mawakin jam'iyar APC Rarara ta ziyarci jihar Kebbi, amma ba'a saki Mawakan ba, duk da yake Rarara ya nuna karara rashin gamsuwa da matakin wakan batanci da Mawaka APC na jihar Kebbi suka yi.
Mujallar ISYAKU.COM ta samo cewa, an saki Mwakan ne ranar 29 kafin ranar 30 ga watan Janairu, kasancewa ranar da Kotu za ta yanke hukunci kan ko za ta yarda da takkardar neman beli da Lauyoyin Mawakan suka gabatar a gabanta.
Tuni labarin sakin Mawakan ya bazu a sako sako na jihar Kebbi, lamari da Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa ya kara daukaka daraja, da kimar masu karan Mawakan na jam'iyar APC na jihar Kebbi a idanun talakawa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari