Yombe ya karbi Isyaku a ofishinsa, duba abin da ya ce

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Samaila Yombe Dabai, ya yi kira ga masu shafukan intanet mallakin kansu a jihar Kebbi su kasance masu hakuri tare da bayar da labarai masu inganci domin ci gaban al'umman jihar Kebbi da Najeriya.

Yombe ya yi wannan bayani ne lokacin wata ziyara da Isyaku Garba Zuru, Mawallafin Mujallar ISYAKU.COM ya kai a ofiishinsa da ke garin Birnin kebbi ranar Litinin.
Yombe ya ce " Kafar sadarwa na zamani ko intanet, sabbin hanyoyi ne na isar da bayanai da sakonni na Gwamnati, kasuwanci,kimiyya, fasaha, ko kimiyyar aikin gona da ci gaban al'umma, wanda hakan ya bayyanar da muhimmancinsu a ci gaban zamani".

Isyaku Garba Zuru ya ce " Na zo ne in ziyarci Baba na, kuma babban yayana, domin nuna farin cikina bisa yadda yan asalin kasar Zuru suka sami kulawa a sabbin nade nade da aka yi a jihar Kebbi yan kwanakin baya. Wannan ya dace da lokaci bisa manufa da ci gaban jihar Kebbi a daidai wannan bagire. Tare da fatar wadanda suka sami mukamai a wannan Gwamnati za su amfani jama'ar kasar Zuru a ko ina suke a fadin jihar Kebbi da Najeriya baki daya".
Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe, tsohon soja ne mai mukamin Kanar a zamaninsa, kuma matukin jirgin sama, wanda ya mallaki kananan jiragen sama guda biyu a yanzu, haka zalika masani fasahar tsarawa, tare da hada sassan motoci zuwa kowane irin fasali.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN