Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a yanar gizo, ya nuna yadda wani DPO na yansanda ya dinga dambe tare da kokowa tare da wani matuki Adaidaita sahu, ko Keke napep a Uratta da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa.
Wata ganau ba jiyau ba mai suna Frankline Tonichukwu Ibe, ta ce lamarin ya faru ne bayan matuki Adaidaita sahu ya bugi motar DPO, bayan ya yi karo da motar DPO daga baya.
Sakamakon haka, DPO ya fito kuma lamarin ya kai ga cacan baki,daga bisani sai dambe ya kaure tsakanin DPO da mai Adaidaita sahu.
Daga bisani yansanda sun zo suka fara dukan mai Adaidaita sahu, DPO na marinsa, wani dansanda kuma ya dinga harba bindiga domin jama'a su watse.
Kalli bidiyo:
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari