Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa sakamakon kashe mijinta Bilyaminu

Yar Najeriya Maryam Sanda, ta kasa rike hawayenta da suka yi da zubowa sakamakon kuka da ta dinga yi ba kakkautawa bayan Alkalin babban Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar ratayeta har ta mutu.
 
Alkalin Kotun Jastis Yusuf Halilu ya same ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello.
 
Yanke hukuncin ke da wuya, Maryam Sanda ta fashe da kuka, kuma ta kasa iya rike kanta, amma a bayyane yake cewa Lauyanta, tare da jami'an Kurkuku, sun yi ta lallashinta kafin daga bisani aka fita da Maryam da gudu daga cikin Kotu, yayin da Manema labarai suka bita da gudu suna daukan hotuna da bidiyo kafin a sakata a cikin mota.

Alkalin Kotun ya ce tana da dama ta daukaka kara.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN