Sun kashe dan kasuwa suka yi gunduwa da gawarsa bayan sun kwace dukiyar N900m

Yansandan birnin tarayya Abuja sun kama wasu mutane uku da suka kashe dan kasuwa mai suna Chief Ignatius Odunukwe, suka sassare jikinsa gunduwa gunduwa kuma suka saka shi a cikin wata jaka suka jefar a daji.

Wadanda suka kashe dan kasuwan sun je wajensa ne bisa yaudara cewa masu sayen gidaje da filaye ne, kasancewa dan kasuwan yana son ya sayar da wani filinsa a kan kudi naira miliyan dari tara (N900m).

Bayan dan kasuwan ya basu takardun filin ne sai suka kashe shi. Yansanda sun gano gawar tare da wadanda suka kashe shi yayin gudanar da bincike. Mazauna unguwar da aka gano gawar dan kasuwan ne suka shaida wa yansanda.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN