A London Buhari ya zayyana alhairan rufe bodar Najeriya

Rahotun Legit Hausa

A ranar Asabar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rufe iyakokin kasar nan ya zama abin farin ciki ga manoman kasar nan. Rufe iyakokin kasar nan ya rage shigo da amfanin gona tare da makamai. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a taron da yayi da wasu 'yan Najeriya a Ingila.

Ya kara musu bayanin cewa za a yi amfani da rufe iyakokin wajen jaddada tsaro da tattalin arzikin kasar nan. Ya jaddada cewa ba a rufe iyakokin Najeriya ba don a muzgunawa makwabtan kasar nan ba, amma sai dai don a karfafa tsaro da tattalin arzikin kasar nan. Shugaban kasar ya danganta rufe iyakokin da aka yi da cigaba da aka samu ta fannin abinci a damina uku da suka gabata.

Ya kara da cewa, rage farashin taki da gwamnatin tarayya tayi zuwa kashi 50 ya matukar taimakawa. Shugaban kasar ya jinjinawa 'yan Najeriya da ke kasashen ketare a kan rawar da suke takawa fannoni da dama na kwarewarsu.

A yayin da shugaban kasar ke bayanin nasarorin da aka samu a bangaren habaka tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma samar da tsaro, shugaban kasar ya ce kullum ana karfafa guiwar matasan kasar da su koma gona kuma su cigaba da rayuwa mai tsafta da mutunta kai.

A bangaren tsaro, ya ce "sanannen abu ne cewa sai da tsaro mai inganci za a iya mulki cikin kwanciyar hankali. Hakan kuwa yayi babbar illa ga yankin Arewa maso gabas na kasar nan." A yayin magana kan yaki da rashawa, shugaban kasar yace rashawa ta yi muguwar illa ga sunan kasar nan da kuma tattalin arzikinta.

Gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen karbo kadarori da kudaden kasar nan da wasu marasa kishin kasa suka wawura.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN