Mutane tara sun mutu bayan wata motar bas ta ci karo da wata mota a garin Ijebu Ife da je kan titin Ore Ijebu zuwa Ode Sagamu a jihar Ogun.
Hakazalika wasu mutum uku sun sami munanan raunuka.
Kwamandan kiyaye hadurra ta kasa na jihar Ogun, Clement Oladele ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce motar ta kama da wuta ne da misalin karfe 3:20 na rana sakamakon taho mu gama da motar bas kirar Toyota Hiace dauke da fasinja 19 ta yi da wata mota, yayin da take cikin tafiya a kan titi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari