Sakamakon kama wasu Mawaka biyu da jami'an tsaro suka yi, kuma suka gabatar da su a gaban babban Kotun Majistare da ke garin Birnin Kebbi bayan Alkalin Kotun Samaila. K. Mungani ya bayar da Warantin kama sauran Mawaka 15 daga cikin 18 da Gwamnan jihar Kebbi ya yi kararsu bisa abin da ya kira bata sunansa,mutunci da martabarsa da Mawakan suka yi a cikin wata wakar batanci da suka rera.
Sakamakon wani takaitaccen bincike da muka gudanar ya nuna cewa sauran Mawakan sun tsere gaba daya daga jihar Kebbi zuwa wasu jihohin Najeriya, wasu kuwa, ana kyautata zaton cewa sun shilla zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.
Bayanai sunce wani Mawaki mai suna Nafiu Gwadangaji, ya dawo ranar Talata, bayan matarsa ta haihu, kwatsam ranar Laraba sai jami'an tsaro suka kama shi, suka kai shi Kotu, daga bisani Kotu ta tasa keyarsa zuwa Kurkuku tare da sauran Mawaka 4 da aka gurfanar a gabanta har zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu ranar da Kotu za ta sake zama domin ci gaba da shari'a.
Hakazalika, an kama Malami Jabbi Bunza, aka hada su da Musa Na' Allah (Mai shinkafa), Ibrahim S. Fulani da Muhammad Sani (MSani).
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari