Ashsha: Wani saurayi ya rataye kansa a bishiya ya mutu a jihar Katsina

Al'umman garin Jibia a jihar Katsina sun ga wani abin mamaki bayan wani saurayi ya rataye kansa a wata bishiya har ya mutu.

Rahotanni sun ce al'umman garin sun ga gawar saurayin ne tana lilo daga bishiyar, amma babu wanda ya san yadda aka yi har wannan saurayi da ba a ambato sunansa ba ya kashe kanshi.

Sai dai wata majiya a garin ta ce an lura cewa saurayi ya yi ta fama da matsanancin rashin kudi da talauci kafin wannan lokaci da ya mutu.

Tuni jami'an ma'aikatan lafiya suka dauke gawar saurayin suka tafi da ita Asibiti.
 

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN