Da duminsa: Alhassan Ado Doguwa ya sake lashe zabe

Rahotun Jaridar Legit Hausa

Hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta alanta Alhassan Ado Doguwa, matsayin zakaran zaben mai-mai na mai wakilatan mazabar Tudun Wada/Doguwa a majalisar wakilan tarayya. Baturen zaben, Farfesa Mansur Bindawa, ya bayyana cewa Ado Doguwa na jam'iyyar All Progressives Congress,
APC, ya samu kuri'u 66,667 yayinda abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya samu kuri'u 6,323 .

Za ku tuna cewa a ranar 4 ga Nuwamba, 2019, kotun daukaka kara dake zauna a Kaduna ta fitittiki Ado Doguwa wanda yake shugaban masu rinjaye a majalisar, tun ta bada umurnin sabon lale.

Mun kawo muku rahoton cewa Tsohon dan majalisan wakilan tarayya, AbdulMumini Jibrin, ya fadi ba nauyi a zaben mai-mai da aka gudanar a mazabar Kiru/Bebeji na jihar Kano. Jibrin wanda yake dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya sha kasa hannun abokin hamayyarsa Alhaji Ali Datti Yako, na Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar 25 ga Junairu, 2020.

Baturen zaben, Farfesa Abdullahi Arabi, ya ce Ali Datti ya samu kuri'u 48,641 yayinda AbdulMumini Jibrin ya samu kuri'u 13,507.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN