• Labaran yau


  Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci

  Rahotun Legit Hausa

  Daily Nigerian ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa a Filato sun kai hari a wasu unguwannin Fulani a jihar inda suka banka wa gidaje 23 wuta har da wani masallaci.

  Ana yi wa harin kallon ramuwar gayya sakamakon kisar gilla da aka yi wa wasu 'yan jihar 13 da ake zargin makiyaya dauke da bindigu ne suka aikata a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos na jihar ta Filato.

  A cewar rahoton, kungiyar makiyaya ta of Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN ta wata kungiyar Fulani, GAN Allah Association sun tabbbatar da afkuwar harin yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata 28 ga watan Janairu.

  Shugaban MACBAN, Isa Bappa ya ce, "Muna kira ga hukumomin tsaro su rika gudanar da aikinsu kafin su yi fitar da sanarwar."

  "Abin takaici ne yadda wasu matasa na Kwatas suka kai wa Fulani harin ramuwayar gayya a unguwannin su. Dukkan hare-haren biyu da aka kai abubuwan bakin ciki ne. "Muna kira ga hukumomin tsaro a jihar da suyi gaggawar kamo wadanda suka kai hare-haren biyu," inji shi.

  A bangarensa, gwamnan Filato, Lalong Simon ya bayar da umurnin kama wasu shugabannin kungiyoyin Fulani da shugabanin wasu garurruwa nan take.

  Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan 'yan sanda na jihar Isaac Akinmoyede yayin taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka hada da masu rike da sarautun gargajiya, shugabanin Fulani da sauran shugabanin al'umma da shugabanin addini da aka gudanar a ranar Talata 28 ga watan Janairu.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matasan Filato sun kai hari unguwar Fulani, sun kone gidaje da masallaci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama