• Labaran yau


  Kotu ta sake tura mawakan jihar Kebbi Kurkuku, an sake kama mawaka 2 sun zama 5

  Jama'a a wajen Kotun Majistare Birnin kebbi
  Wasu mawaka da ake zargi da yin wakan batanci tare da cin zarafin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu, sun sake gurfana a gaban Kotun Majistare a garin Birnin kebbi karkashin Alkalancin Samaila K. Mungadi.

  Da karfe 2:32 na rana aka fara shari'ar bayan Lauyoyin mai kara sun gabatar da kansu wadanda suka hada da Lagalo Dan Lagalo da E.A Wasagu, amma babban Laya Y.C Maikyau (SAN) bai halarci zaman Kotun ba a yau.
  Barista A.A Fingilla Lauyan kare hakkin bil'adama

  Daga bangaren Lauyoyi masu kare Mawakan, sun hada da Barista A.A Fingilla, Sanusi Sani, da Nuruddeen Muhammed, sai kuma Nura Bello.

  Mawaka da suka gurfana a Kotun sun hada da Musa Na' Allah (Mai shinkafa), Ibrahim S. Fulani da Muhammad Sani (MSani) .

  Motocin Kurkukun jihar Kebbi da aka sa Mawakan
  Ana cikin shari'ar ne sai aka kama Malami Jabbi Bunza aka kawo shi gaban Kotu. Hakazalika an sake kamo Nafi'u Gwadangaji, aka kawo shi cikin Kotu wanda ya kawo adadin Mawakan da aka kama suka zama biyar.

  Lauyan Gwamnati Lagalo ya jajirce a kan cewa dole ne a kawo sauran Mawakan, ya kuma bukaci Kotu ta tasa keyar Mawakan zuwa Kurkuku har a kamo sauran Mawakan.
  Lauya Nuruddeen Muhammed daya daga cikin Lauyoyi masu wakiltar Mawakan

  Amma Lauyoyin Mawakan Barista Fingilla, Nuruddeen, da Nura sun nace a kan cewa a ci gaba da shari'ar, tare da bukatar Kotu ta bayar da belin Mawakan. Tun farko dai, Fingilla da Nura, sun shaida wa Kotu cewa sun gabatar da bukatar neman Kotu ta bayar da belin Mawakan a rubuce tun ranar 13 ga watan Janairu.

  Bayan doguwar muhawara tsakanin Lauyoyin Gwamnati da na Mawakan, wanda aka fara daga karfe 2:32 na rana har zuwa 6:42 na yamma. Alkalin Kotun Samaila Mungadi, ya sa ranar 30 ga watan Janairu domin yanke hukunci a kan zancen ko Kotu za ta bayar da belin Mawakan bisa bukatar Lauyoyinsu.
  Jama'a wajen Kotu bayan daga shari'ar Mawakan jihar Kebbi

  Ya kuma sa ranar 3 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari'ar mawakan. Daga bisani Kotu ta yi umarnin cewa a kai Mawakan Korkuku har wannan rana.

  Rahotun Isyaku Garba Zuru

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta sake tura mawakan jihar Kebbi Kurkuku, an sake kama mawaka 2 sun zama 5 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama