• Labaran yau


  An kashe kasurgumin mai garkuwa da mutane 'Yunusa Boka'


  Rahotun Legit Hausa

  Hukumar yan sandan jihar Katsina ta alanta hallaka Yunusa Boka, kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ya ke aika-aikansa a Danmusa da karamar hukuma Kankara ta jihar.

  Kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya bayyana hakan ne a jawabin da saki ranar Laraba inda yace an hallaka Yunusa Boka ne a musayar wuta da yayi da jami'an tsaro a dajin Gwarzo, karamar hukumar Matazu ranar Talata.


  Kakakin, Gambo Isah ya kara da cewa gamayyar jami'an yan sanda, Sojoji da tubabbun yan bindiga suka kai harin kuma sun ceto wata mata da jaririnta mai wata bakwai da haihuwa.

  Yace: "Bisa ga rahoton leken asiri, an shirya gamayyar jami'an yan sanda, Sojoji da tubabbun yan bindiga domin kai farmaki mabuyar masu garkuwa da mutane a dajin Gwarzo, karamar hukumar Matazu"

  "Bayan musayar wuta da yan bindigan, an samu nasarar kashe kasurgumin mai sace mutane, Yunusa Boka, wanda ya addabi al'ummar yankin."


  "Hakazalika an ceto wata mata Firdausi Yusuf, yar kauyen Burunkuza da jaririnta dan watanni 7, Amin Y Gambo ya ce an garzaya da matar da yaronta asibitin Danmusa domin duba lafiyarsu kuma tuni an mayar da su wajen yan'uwansu. Ya yi kira ga mutan jihar su taimakawa jami'an tsaro da labarai kan yan tada zaune tsaye a unguwanninsu.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe kasurgumin mai garkuwa da mutane 'Yunusa Boka' Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama