Duba yawan mutane da basu iya karatu ko rubutu a Najeriya

Fiye da mutane miliyan 60 ke rayuwa cikin jahilcin rashin iya rubutu ko karatu a kowane irin yare a Najeriya . Hukumar kula da ilimin manya da ilimin bai daya na kasa watau National Commission for Mass literacy, Adult and Non-Formal Education ta yi wannan hasashe inji jaridar Daily Trust.

Babbabn Sakataren ma'aikatan, Abba Abubakar Haladu ne ya ambato haka, a lokacin wani taron ma'aikatan a birnin Abuja a karshen mako.

Haladu ya kara da cewa duk da kalubalen da Najeriya ke fama da shi na yara da basu ci gaba da makaranta, ya ce hakazalika kasar na fama da kalubalen yawan wadanda basu iya karatu ko rubutu.

Ya kara da cewa wannan babban barazana ne ga ci gaban Najeriya, duba da miliyoyin matasa da lamarin ya shafa.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN