KISHI ya sa wata mata ta tunkude kishiyarta da goyo ta fada cikin rijiya

Rahotun Legit Hausa

Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wata matar aure, Hauwa Lawal, kan laifin jefa kishiyarta, Zuwaira Sani, da dan goyonta, Mustafa Gambo, cikin rijiya a karamar hukumar Rano ta jihar. Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da damketa a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi.

Haruna ya bayyana cewa hukumar ta samu rahoto ranar Juma'a cewa matar mai suna Hauwa a kauyen Rurum dake karamar hukumar Rano ta tunkuda dan kishiyarta cikin rijiya. Bayan aikata wannan aika-aika, Hauwal Lawal, ta arce daga gidan kuma aka fara nemanta ruwa a jallo. Haruna yace misalin karfe 1:17 na daren Asabar jami'an atisayen Puff Ader sukayi ram da ita.

Yace: "Matar ta samu sabani da kishiyarta. Kawai sai suka fara fada a cikin gidan, sai ta jefa kishiyarta dake goye da danta mai watanni 18 da haihuwa, Mustafa Gambo, cikin rijiyan dake gidan." "Daga baya aka ciro matar da 'danta daga cikin rijiyan kuma aka garzaya da su asibitin Rano inda aka tabbatar da mutuwar matar amma 'danta goyonta ya rayu kuma an sallamesu daga asibiti." "Muddin muka kammala bincike, za'a gurfanar da ita a kotu."

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN