Gwamnatin jihar Bauchi ta gano ma'aikatan gwamnatin jihar guda 596 da suka mutu kuma ana biyan albashinsu da alawu har tsawon shekaru.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamnatin jihar Bauchi ta bankado fiye da ma'aikata 41,448 da ke karbar albashi daga gwamnatin jihar alhalin basu da lambar tantancewa na Banki watau BVN.
Gwaman jihar Bauchi Bala Muhammed, ya nada wani kwamiti da zai yi bincike a kan lamarin. Shugaban kwamitin Adamu Gumba ya shaida wa manema labarai sakamakon tantancewa da suka yi.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari