Kiri kiri da rana tsaka wani da'u fataken dare ya gamu da hukuncin katti, karanta dalili

Dubun wani mutum mai suna Nator Lartue ta cika bayan matasa a garin Korinya da ke karamar hukumar Konshisha a jihar Benue sun kashe shi kuma suka banka wa gawarsa wuta ta kone kurmus bayan sun zarge shi da aikata fashi da makami tare da yan kungiyarsa.

ISYAKU.COM ya samo cewa Nator wanda ake wa inkiya da sunan Natoo ya kwace kudi da dukiya daga hannun wani dan kasuwa mai suna Mr Terna wanda ake wa inkiya da Spanner, lokacin da ya tashi daga shago kan hanyarsa ta komawa gida da dare tare da diyarshi wacce ke duba masa shago.

Mun samo cewa diyar ta sami tserewa lokacin da yan fashin suka tare Mr Terna, sun kwace komai a hannunsa kuma suka yi yunkurin halaka shi, ammam sai wasu daga cikinsu suka bukaci a kyale shi domin gobe a cewar majiyarmu.

Bayan labari ya bazu a gari, sai yansandan sashen SARS na yansandan garin Korinya suka kama Nator, amma sauran yan kungiyarsa sun tsre.

Daga bisani matasan garin Korinya sun afka suka kwace Nator daga wajen yansanda, suka kaishi daji suka kasheshi, kuma suka banka wa gawarsa wuta ta kone kurmus.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN