![]() |
Photo credit: Channels TV |
Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.
Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.
Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara. Hakazalika, kotun ta umurci hukumar INEC ta kwace shahadar nasarar zabe daga hannun Emeka Ihedioha kuma ta mikawa Hope Uzodinma na jam'iyyar APC.
A cewarta: "An zabge Kuri'un da Sanata Hope Uzodinma na APC ya samu a rumfunan zabe 388. Saboda haka mun bada umurnin dawo masa da kuri'un da ya samu a wadannan rumfuna 388 kuma hakan ya nuna cewa Emeka Ihedioha bai samu kuri'u mafi rinjaye ba."
"Mun yi watsi da sanar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Imo." "Bayan hakan, mun alanta mai kara (Hope Uzodinma) matsayin wanda ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben jihar Imo da ya gdana ranar 9 ga Maris , 2019."
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari