Wata motar daukan gawa wacce ta dauko gawar wata mata mai suna Mrs. Onyemata, ta kama da wuta kuma ta babbake a gefen titi a kan haryar zuwa Mutuwaren Mercy a garin Umologhu da ke Obawo a jihar Imo.
Lamarin ya faru ranar 11 ga watan Janairu a babban titin Owerri zuwa Umuahia.
Sai dai an sami nasarar ceto gawar kafin ta kone dai dai lokacin da motar ta kama da wuta sakamakon yoyon fetur lokacin da motar take tafiya.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari