• Labaran yau


  Jama'an gari sun kashe makwabcinsu suka banka wa gawarsa wuta, karanta dalili

  Wani mutum ya rasa matarsa wacce uwa ce ga yara 6, 3 maza 3 mata, bayan ya harbe ta da bindiga sau biyu, lamari da ya yi sanadin mutuwarta a garin Nkporo da safiyar ranar Litinin.
  Wannan mutum mai suna Kalu Ilum na unguwar Etitiama da ke Nkporo, wanda garin mataimakin Gwamnan Abia ne, ya kashe matarsa da misalin karfe 7. Sai ya gudu ya yi tsalle ya fada cikin wani rijiya.

  Jama'a sun lallashe shi ya fito da kanshi, sai suka afka masa da duka suka kashe shi, kuma suka banka wa gawarsa wuta, daga bisani suka rushe gidansa.

  Rahotanni sun ce mijin matar ya yi wa yanuwan matar barazanar cewa zai harbe ta da bindiga ya kasheta, kuma ba abin da zai faru. Hakazalika bayanai sun ce matar ta yi kokarin kashe aurenta da shi saboda yawan cin mutunci da tashin hankali da yake yi mata.
  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jama'an gari sun kashe makwabcinsu suka banka wa gawarsa wuta, karanta dalili Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama