Kasar Iran ta saka ladan Dala miliyan tamanin $80 ga duk wanda ya halaka shugaban Amurka Donald Trump. Wannan ya biyo bayan kalaman Trump na cewa Amurka za ta kai wa kasar Iran mumunar hari matukar ta taba maradunta a harin ramuwar gayya.
Gidan Talabijin na kasar Iran ta bayar da sanarwar haka , tana mai cewa " Iran tana da mutane miliyan 80 bisa kididdigan yawan jama'an kasar Iran. Idan jama'a za su tara dala daya kowannensu za a sami dala miliyan tamanin $80 kenan domin bayarwa ga duk wanda ya halaka Trump"
Wannan ya zo daidai da lokaci da ake gudanar da jana'izan Janar Qassem Soleimani da kasar Amurka ta kashe bisa umarnin shugan Amurka Donald Trump.
Jiragen tuka kanka na kasar Amurka sun harba makami mai linzami a kan motar Janar Qassem Soleimani wanda haka ya zama sanadin ajalinsa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari