• Labaran yau


  Hotunan yadda mata suka dinga kuka suna birgima a titi bayan cire Ihedioha daga mulki

  Magoya bayan tsohon Gwamnan jihar Imo Emeka Ihedioha, sun bazama kan titin babban birnin jihar, watau Owerri , ranar Lahadi suna la'antar hukuncin Kotun koli da ya kori Ihedioha daga kujerar mulkin jihar.

  Ranar Talata da ta gabata ne Kotun koli ta Najeriya ta soke nassarar da INEC ta ba Emeka Ihedioha na jam'iyar PDP, ta kuma mika wa Hope Ozodinma na jam'iyar APC.

  Magoya bayan Ihedioha sanye da bakaken tufafi, sun kwanta a kan titi maza da mata suna kuka, tare da birgima. Wasu kuma suna rike da kwalaye da aka rubuta " Muna bukatar ya dawo" da " An halaka dimokaradiya"  sai " Ihedioha dai muka sani" da sauransu.


  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan yadda mata suka dinga kuka suna birgima a titi bayan cire Ihedioha daga mulki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama