Yanzun nan: Kotun koli ta jaddada wa Gwamnonin Adamawa da Benue kujerarsu

Kotun koli ta Najeriya ta jaddada wa Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umar Fintiri kujerarsa a zaben 9 ga watan Maris 2019, bayan ta yi watsi da karar da dan takarar Gwamna a jam'iyar APC Muhammadu Bindow ya shigar, inda ya kalubalanci zaben Fintiri na jam'iyar PDP a zaben Gwamnan jihar Adamawa.

Hakazalika, Kotun ta yi watsi da kara da aka shigar a kan zaben Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ta kuma jaddadad masa kujerarsa, tana mai cewa masu kara sun kasa gamsar da Kotu kan da'awarsu a kan Ortom.

Alkalai bakwai ne suka yi hukunci a kan wannan shari'a, wanda suka hada da:

1. Hon. Justice Olabode Rhodes-vivour

2. Hon. Justice Nwali Sylvester Ngwuta

3. Hon. Justice musa Dattijo Muhammad

4. Hon. Justice Amiru sanusi

5. Hon. Justice Amina Adamu Augie

6. Hon. Justice Paul Adamu Galumji

7. Hon. Justice Uwani Musa Aba Aji

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN