Har yanzu mawakan APC a jihar Kebbi na gidan Kurkuku

Yayin da ya rage mako daya kafin ranar da za a sake gabatar da Mawakan jihar Kebbi da Gwamnan jihar Kebbi ya yi karansu a gaban Kotun Majistare a garin Birnin kebbi, bisa zargin rera wakar batanci da ya keta mutunci da martabarsa da Mawakan suka yi.

ISYAKU.COM ya samo cewa, duk da yake Lauyoyin Mawakan sun gabatar da takardar neman belin Mawakan kamar yadda Kotu ta yi umarni a zamanta na baya. Sai dai har yanzu Mawakan na Kurkuku.

Tun ranar Litinin ne dai ake ta rade radin cewa an bayar da belin Mawakan guda uku da Kotu ta tasa keyarsu zuwa Kurkuku. Sai dai ISYAKU.COM ya binciko cewa ba a bayar da belin Mawakan ba kawo yanzu da aka rubuta wannan rahotu.

Mawakan za su sake gurfana a gaban Kotu ranar 22 ga watan Janairu 2020 domin ci gaba da fuskantar shari'a da ake yi, sakamakon kara da Gwamna Atiku Bagudu ya shigar a kansu bisa zargin wakar cin zarafinsa a wakar da suka rera.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN