Gobara ta lakume wani gida a Tudun wada Birnin kebbi

Allah ya jarrabi wasu bayin Allah bayan gobara ta lashe gidansu da safiyar Laraba 15 ga watan Janairu da misalin karfe 11:30, a unguwar Tudun wada kusa da babban Masallacin jihar Kebbi watau Central Moaque a garin Birnin kebbi.

Matasan unguwan sun taka rawar gani wajen bayar da gudunmuwa domin kashe gobaran ta hanyar amfani da ruwa a cikin bokitai suka hau katangar gidan suna zuba ruwa.

Hakazalika matan aure tare da yanmata makwabta sun dinga debo ruwa a bokitai ana mika wa jama' a da ke kashe gobarar kafin isowar motar farko ta hukumar kashe gobara ta jihar Kebbi wanda jami'anta suka dukufa wajen kashe gobarar tare da matasan unguwa.

Mun kula da yadda makwabta mata da maza ke hawaye yayin da gobaran ke tsakar ci tare da turnukewar hayaki.

Bisa ga alamu babu asarar rai a wanna gobara, sai dai ba a fita da komai ba kamar yadda muka lura.

Mun kuma samo cewa Allah ya yi wa mai gidan rasuwa tun shekaru da dama da suka gabata, amma iyalinsa ke cikin gidan kafin aukuwan wannan ibtila'in gobara.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN