Ga duk wanda ya ke kallon shirin Kwana Casa’in, ya san cewa Surayya
Aminu wadda a ka fi sani da Rayya tauraruwar ta na haskawa a cikin
shirin kasancewar matsayin ta a ciki shirin na fitowa a munafuka da kuma
mai wauta wanda hakan ya sanya ta yi suna sosai.
Majiyar mu ta Northflix ta sami damar tattaunawa da jaruma Rayya,
wato Surayya Aminu mu ka ji ta bakin ta in da ta fara da tarihin rayuwar
ta kamar haka.
“Ni suna na Surayya Aminu, kuma an haife ni ne a garin Ikeja da ke
jihar Legas, amma na girma ne a jihar Kaduna, na yi karatun firamare da
Sakandare da na Islamiyya duk a garin Kaduna. A yanzu kuma ina karatun
Digiri a Jami’ar Karatu daga gida wato (NOUN)”.
Dangane da yadda ta samu kan ta kuwa a matsayin jaruma cewa ta yi
“To ni dai tun ina karama na ke da burin na ga na yi harkar fim, amma
dai abin da ya ba ni karfin gwiwar shiga shi ne saboda ina so na ga na
karanta Mass Communication wato karatun koyon aikin jarida, to wannan
burin kusan dai shi ne abin da ya ja ra’ayi na wajen shiga harkar fim.
Kuma wanda ya yi mini hanyar shigowa shi ne Nura M, Sultan a nan Kano da
kuma Nazir Adam Saleh, wadannan su ne su ka zama hanya ta ta shigowa
harkar fim”.
Daga lokacin da Surayya ta shigo harkar fim zuwa yanzu ko ta yi fina-finai kamar nawa?
“To
fina-finan da na yi ba su da yawa, domin ban dade da shigowa harkar ba,
amma duk da haka fina-finan da na yi za su kai biyar, kuma a yanzu da
za a tambaye ni wanda na fi so a cikin su to gaskiya na fi son Kwana
Casa’in, saboda shi ne Duniya ta sanni, don haka na fi son sa a cikin
dukkan fina-finan da na yi.
Don gaskiya na ji dadi sosai da na samu
kaina a cikin shirin Kwana Casa’in, kuma na ji dadin irin fitowar da na
ke yi irin ta munafurci da rawar kai da sauran su domin hakan ina jin
dadin fitowa da na ke a cikin wannan shirin babu abun da zan ce sai
godiya ga Allah “.
Ko jaruma Surayya akwai wata jaruma da ta ke burge ta kuma ta ke koyi da ita a salon fim?
“’A gaskiya ni babu wata jaruma da na ke koyi da ita, kawai dai ana
ba ni role ne, ni kuma ina hawa, don haka ba maganar koyi da wata ba
ne.” inji Rayya.
Daga karshe ko wanne buri Surayya ta ke da shi?
Sai ta karkare zancen ta da cewa “Buri na dai na samu shiga duniya
ta sanni, kuma a yanzu Alhamdulillahi babu abun da zan ce sai godiya ga
Allah, kuma ina godiya ga wadanda su ka yi min hanya, sannan masoya na
ina yi musu fatan alheri, Allah ya bar mu tare.” A cewar jaruma Rayya.
#northflix
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari