Gobara da ta kashe dan kasuwa: Kwamishinan yansandan jihar Kebbi ya yi gargadi

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta yi kira ga jama'ar jihar Kebbi cewa su kaurace wa ajiye man feture tare da wasu ababe da za su iya haddasa gobara a gidajensu. Kwamishina Ogunbiade Oluyemi Lasare, ya ambato haka a wata takarda da aka aike wa manema labarai a garin Birnin kebbi ranar Litinin.

Ya ce rundunarsa ta sami rahotun tashin gobara a garin Yauri da Kalgo, lamari da ya yi sanadin mutuwar Alhaji  Haruna Tondi Ital.

Kwamishinan ya bukaci jama'ar jihar Kebbi su kai rahotun duk wanda, ko mutane da aka gani suna ajiye man fetur ga yansanda domin kauce wa aukuwan gobara musamman a wannan lokaci na hunturu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari