Wani bola da ke kara fadada a yamma maso kudancin katangar Sakatariyar Haliru Abdu, kuma a gefen Masallacin Juma'a na Haliru Abdu, yana kara zama barazana ga tsabta da kuma lafiyar al'umma da ke wannan unguwa a cikin garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi.
Yanzu haka, wannan bola yana kara fadada, duk da yake, yan jari bola kan kone tarkacen bolan lokaci zuwa lokaci. Lamari da ke haifar da tashin hayaki da ya hada da na busashen bahaya na bil'adama, audugan tarae hailar mata da robobi, lamari da masana suka ambato cewa hayakin illa ne ga lafiyan makwabtan wannan bola.
Sai dai bincike da muka gudanar, ya nuna cewa rashin tsayayyen bola a wannan unguwa, shi ya sa ake amfani da wannan wuri a matsayin bola.
TSOKACI
Mujallar ISYAKU.COM yana kira ga hukumomin da hakkin kula da wannan bola ko tsabtan gari ya ta'allaka a kansu, cewa su kawo dauki domin ganin an tsabtace wannan wuri.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari