Yadda wata kungiya ta sa farin ciki a rayukan bayin Allah a wata jihar arewa

Kungiyar taimakon gajiyayyu mai zaman kanta na kasa watau Equity Destitute Child Right and Welfare Initiative karkashin jagorancin shugabanta na kasa Hajiya Fatima Muhammed Kabir tare da mambobin kungiyar maza da mata, ta gudanar da ziyarar bayar da kyautan kayakin masarufi ga mabukata a Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi da garin Gwadangaji.

Kungiyar ta bayar da kyautar takalma da kayan masrufi ga daruruwan Almajirai a Birnin kebbi da Gwadangaji, hakazalika ta kai ziyara gidan Gyara halinka da gidan Marayu a garin Birnin kebbi inda ta bayar da kyautar kayakin masarufi da takalma ga yara da ke gidajen guda biyu.

Hajiya Fatima ta ce  " Kungiyarsu tana da mafufar taimaka wa gajiyaayyu, Marayu,  Almajirai da marasa galihu. Kungiya ce da ke maraba da kowaa domin akwai mutane daga ayyukan rayuwa daban daban da suka hada da Likitoci, Laiyoyi, yan kasuwa, yan Jarida da sauransu. Hakazalika akwaai Musulmai da Kiristoci, kungiya ce da ta kunshi kowa domin aiwatar da jinkai ga al'umma".
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
 Facebook.com/isyakulabari
 Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN