Duba wani alhairi da dan kabilar Igbo ya yi a kauyensu da babu irinsa a kauyen arewa

Dan karamin kauyen Umuchukwu wanda a da ake kira Nkerechi da ke karamar hukumar Orumba ta yamma a jihar Anambra, digo ne kawai a taswiran Najeria. Wannan gari yana da mazauna cikinsa mutum 3000, amma gari ne da ke da gini mafi tawo a kar Igbo.

Wannan gini yana da hawa 15 wanda wani Likita mai suna Dr. Godwin Maduka dan asalin wannan gari ya gina a cikin garin. Dr Maduka Likita ne wanda shi ne babban jami'in gudanarwa kuma babban Daraktan Likitanci na  Pain Institute and Medical Centre da ke Las Vegas wanda shi ne cibiyar maganin ciwon radadi a Naveda da ke kasar Amurka.




Wannan bene a kauyen Umuchukwu, zai kasance waje mafi girma da za a dinga gudanar da binciken Likitanci a nahiyar Afrika.


TSOKACI

Wannan ya nuna irin yadda yan kudancin Najeriya suke da kishin kasarsu da kuma jama'arsu bisa manufa a wani lokaci. Koma da miye, wannan Likita ya nuna kishin kauyensu ta hanyar kawo masu ci gaba mai daurewa ba tare da amfani da damar gwamnati ba kamar yadda muka saba gani a kasar arewa inda shugabanni ke amfani da dama na shugabanci suna amfani da dukiyar jama'a domin su gina makarantu ko ababe makamantan haka a garuruwansu.

Abu ne mawuyaci mu gan attajiran mu sun yi irin wannan aiki domin jama'arsu a kasar arewa. Gaba daya a kasar arewa, babu gari mai jama'a 3000 da ke da bene mai hawa 5 balle 15.

Ko miye dalilin da ya jawo haka ? Ku rubuto mana ra'ayinku dangane da wannan lamari da shawara kan yadda ya kamata a yi. LATSA NAN KA RUBUTA RA'AYINKA

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN